abdubodaplatform

@abdubodaplatform
Abdu Boda sanannen suna ne ga duk wani ma,abocin jin wakokin hausa ko kallon finafinan hausa, yana daya daga cikin mawakan da yai matukar shura a kasar hausa, shine mutum na farko da ya fara wallafar da kundin wakokin sa a arewacin nijeriya.

Hafaffan dan jihar katsina ne , ya halacci makarantu da suka hada da UPE kofar primary school, ATC Katsina, Hassan Usman katsina polytechnic, National Film Institute Jos da kuma Jami’ar Yar Adua University dake garin katsina.

Ya kara karatu a fannoni da suka hada da Mass Communication, public Admin, da Cinematography.

Yayi wakoki da dama ciki har da Soyayya soyayya, Duniya ba gidan zama ba, ‘yan nijeriya, Amarya Soyayya, A Sha Ruwa da dai ire iren su.

Ya samu lambar girmamawa ciki har da Honouring Award daga BBC World Entertainment (2014) Award of Honour daga Taskar Ala Global (2014), Gold Award daga International Fair of Khartoum (2003) da kuma DoctoringAward da Jami’ar Ahmadu Bello University Zaria(2017).

Bugu da kari gogan na ku ya samu nadin sarauta a matsayin [BARADE MATASAN AREWA] wadda masarautar Jihar Zamfara ta bashi.